<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>488</hymn_number>
<title>Muna da Murna Yau LW488</title>
<lyrics>[V1]
 1) Mu matan (Sunan gari) muna da murna yau, domin wanna aure, aure mai nasara
 Mu yi murna mataye mu raira godiya muna yin addu'a domin wanna gida.

[V2]
 2) Amariya ki daɗe kina yin addu'a, kina roƙon Allah ya baki mijin aure.
 Yau kin samu amarya ki yi godiya, kina yabon Allah domin Alherinsa.

[V3]
 3) Ango mun san daɗe kana addu'a kan roƙon Allah, ya baka macen aure.
 Yau ka samu ango ka raira Halleluya, kan yabon Allan domin Alherinsa

[V4]
 4) Amarya ki zama kanbi ga mijinki, domin macen kirki kanbi ce ga mijinta
 Kiyi masa biyayya a cikin kome duk, ki kaunace shi kamar yadda Allah ya ce.

[V5]
 5) Ko cikin wahala ko cikin jin daɗi, ko cikin lafiya ko a cikin kunci.
 Ku kasance masu ƙaunar junanku kullum, kuna yin addu'a zaku yi nasara.

[V6]
 6) Samarai da ƴan mata shawar gareku, in zaku aure ku nemi nufin Allah.
 Muna roƙonka, Allah amsa addu'armu, domin matasanmu ka muna ikonka.</lyrics>
</song>